Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A Jihar Kano rahotanni sun ce bangaren Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayan sa sun zabi Alh Ahmadu Haruna Zago a taron da suka gudanar, yayin da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Kabir Gaya ke gudanar da nasu taron inda ake saran zaben Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.
A Jihar Lagos ma, barakar ta fito fili, inda wani bangare na Jam’iyyar ya gudanar da taron sa a Agege, inda ya bayyana Hon Sunday Ajayi a matsayin shugaba, yayin da bangaren Bola Ahmed Tinubu ya amince da jagorancin Hon Cornelius Ojelabi.
A Jihar Ogun an ce wasu ‘Yan bindiga sun kai hari akan masu gudanar da taron jam’iyyar, inda acan ma ake da bangarori biyu tsakanin masu goyan bayan Gwamna Dapo Abiodun da kuma masu goyan bayan tsohon Gwamna Ibikunle Amosun.
A jihar Nasarawa, Jam’iyyar ta amince da sasantawa a tsakanin kananan hukumomin jihar domin raba mukaman ta tsakanin bangarorin jihar.
A jihar Borno, an ga Gwamna Babagana Umara Zulum da wadanda ya gada Kashim Shettima da Ali Modu Sherrif na halartar taron jam’iyyar wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Wadannan shugabannin jam’iyyar da za’a zaba yau ake saran su jagorance ta wajen tsayar da ‘yan takarar zaben Gwamna da ‘Yan Majalisu da kuma shugaban kasar da za’ayi a shekarar 2023.
342/